Thursday, 8 March 2018

Jaruman fina-finan Hausa sunyi dafifi akan hotunan bikin diyar Ganduje suna ta suka

Bayan da akayi bikin diyar gwamnan jihar Kano ya wuce wasu hotunan da ma'auratan suka dauka sun dauki hankulan mutane saboda sumbatar da mijin ya yiwa matarshi. Haka kuma  hotunan sun jawo cece kuce a tsakanin wasu jaruman masana'antar fina-finan Hausa.


Jaruman dai na ganin cewa masu sukarsu idan sunyi wani abu ba daidai ba basu musu adalci domin ga diyar gwamna tayi abinda be dace ba amma musamman malamai babu wanda ya fito Duniya yayi Allah wadai da hakanba, inda suke zargin cewa da sune suka yi irin wannan abu da yanzu Duniya ta dauka anata jifarsu da kalamai kala-kala.

Jarumin da ya fara fitowa fili ya bayyana sukarshi akan wadannan hotunan shine T. Y Shaban inda yace da sune suka aikata irin wannan abu da kaji dirar ayoyi inda har daga baya ya soki abokin aikinshi Nura Hussain da cewa yayi magana akan abinda Rahama Sadau tayi amma yakiyin magana akan diyar Ganduje, duk dadai daga baya ya sake maganarshi.

Tsohon tauraron fina-finan Hausa, Abdulmumin Ilyasu Tantiri ya goyi banayn T. Y Shaban inda shima yake ganin ba'a musu adalci kuma yace yarinya ta jawo musu anin magana.

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Rukayya Dawayya itama ta shiga wannan batu inda tace yarinya ta jawo musu abin kunya.

Haka kuma Zaharadeen Sani Owner shima ya saka hoton na Fatima Ganduje da mijinta Idris Ajimobi na sumbatarta, duk dai cewa bece komi akai ba.

Me bayar da umarni Amisu S. Bono shima ya shiga wannan magana.

No comments:

Post a Comment