Friday, 9 March 2018

Jin labarin za'a mata kishiya, bayan wata biyu da yin aurensu: yasa wata mata ta kona gidan mijinta kurmus

Jin labarin za'a mata kishiya yasa wata mata ta kona gidan mijinta kurmus a jihar Kebbi kamar yanda jaridar The Sun ta ruwaito, Yunus ya rasa tsohuwar matarshi wanda haka yasa yayi sabon aure a watan fabrairun wannan shekarar, indaya auri A'isha, amma shima dai babu alamar zaman lafiya tsakaninshi da matar wannan yasa ya fara shirin yin sabon aure.


Jin labarin haka ya hasala A'isha, cewa wai wata biyu kawai da yin aure tsakaninsu zai yi mata kishiya, ai kuwa sai ta hau dokin zuciya ta cinnawa gidan mijin nata wuta yaci ya cinye.

Rahotanni dai sun nuna cewa an fitar da wasu kaya daga gidan bayan da makwauta suka kawo dauki amma duk sauran wasu kayan mijin sun kone kurmus.

Jaridar ta The Sun ta tuntubi hukumar yansanda akan lamarin amma sun shaida mata cewa babu wani koke da aka kawo musu akan lamarin


No comments:

Post a Comment