Monday, 12 March 2018

Kalli bidiyon Fatima Ganduje na tika rawa da suka jawo mata Allah wadai

Wadannan hotunan bidiyone na rawar da diyar gwamnan jihar Kano, Fatima Abdullahi Umar Ganduje ta tayi kenan a gurin ci gaba da shagalin aurenta da dan gidan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi kenan da akayi acan jihar Oyon, Fatimar tasha suka da Allah wadai daga mutane da yawa musamma  a shafukan sada zumunta dalilin wannan rawa da tayi.


Dama dai Fatimar da mijin nata sun fara shan suka tun a wasu hotunan su da suka bayyana suna sumbatar juna, ashe a wacan lokacin kadan aka gani sai kuma ga hotunan bidiyo sun bayyana Fatimar tana ta tika rawa a gurin bikin nata.

Da yawadai sun bayyana wannan rawa da diyar gwamnan jihar Kanon tayi da tashin tarbiyya.

No comments:

Post a Comment