Sunday, 11 March 2018

Kalli hotunan kamin biki, masu tsafta na diyar Dangote da Angonta

Hotunan kamin biki kenan na Diyar me kudin Duniya Aliko Dangote tare da masoyinta wanda za'a auramata, dan gidan tsohon shugaban 'yan 'yansanda, Jamil MD Abubakar, an fara shirye-shiryen bikin inda akayi liyafar cin abincin dare,kuma hotunan sun kayatar da mutane sosai lura da cewa babu rungume-rungume da aka saba gani a da yawa daga cikin hotunan kamin biki na zamani.Muna musu fatan Alheri da kuma Allah ya sanyawa wannan biki Albarka.

Kamardai yanda aka gani a wani katin gayyatar daurin auren nasu da ya karade shafukan sada zumunta na yanar gizo, za'a daura auren nasu ne ranar 15 ga watan Maris dinnan da muke ciki idan Allah ya kaimu.

No comments:

Post a Comment