Saturday, 17 March 2018

Kalli hotunan marigayi Sanata Ali Wakili jiya a Kano gurin daurin auren Diyar Dangote

Allah sarki Duniya babu tabbas, jiya kenan a garin Kano, gurin daurin auren Fatima Dangote da Jamil MD Abubakar, inda marigayi Sanata Ali Wakili ya halarta, a wannan hoton yana tare da tsohon ministan Abuja, Sanata Bala Muhammad, tauraron me daukar hoto, lilbature yace, marigayin ya kirashi ya bashi wayarshi yace ya daukesu hoto, har wani dattijo yayi wuf ya kwace wayar, sai marigayin yace mishi ka ba wannan yaron ya dauke mu, ba kai nace ba.


Rayuwa kenan, muna fatan Allah ya jikanshi ya gafartamai zunubanshi.
Wannan ma wani hoton marigayinne jiya a Kano.

No comments:

Post a Comment