Wednesday, 7 March 2018

Kalli katin gayyatar daurin auren diyar Dangote

Katin gayyata na daurin auren diyar attajirin dan kasuwa, Fatima Aliko Dangote da dan tsohon shugaban 'yan sanda, Jamil MD Abubakar ya fito,katin ya bayyana cewa ranar 15 ga watan Maris dinnan da muke ciki idan Allah ya kaimu za'a daura auren a garin Kano.Rahotanni dai sun  nuna cewa za'ayi shagalin bikin a Otaldin Eko dake Legas wanda har attajirin Duniya Bill Gates zai halarta da sauran wasu manyan baki kuma wani abu da ke ta kara daukar hankulan mutane akan wannan biki musamman 'yan kudu shine hana kawo giya a gurin bikin wanda mu dama munsan a addininmu ta'ammuli da giya haramunne.

No comments:

Post a Comment