Sunday, 11 March 2018

Kalli kayatattun motocin Angon Fatima Dangote, Jamil MD Abubakar

Jamilu Shine dan fari a gurin mahaifinshi, tsohon shugaban 'yan Sanda Muhammad Dikko Abubakar, Shine wanda zai auri diyar hamshakin attajirin Duniya, Fatima Aliko Dangote wanda yanzu haka an fara shagalin biki kuma idan Allah ya kaimu cikin satinnan da zamu shiga za'a daura musu aure.Jamilu yana da sunan gayu da ake kiranshi dashi watau Jamboy kuma sunan da yake rubuce kenan a jikin lambar motocin alfarma da kece raini da yake hawa kenan, mutum ne me son motocin zamani masu kayatarwa da kuma sanya agoguna masu tsada.

Jamil yana aikin tukin jirgin sama ne, kuma rahotanni sun bayyana cewa akwai lokacin da hadarin jirgin sama ya taba ritsawa dashi amma ya tsallake rijiya da baya. Muna mishi da amaryarshi fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment