Monday, 19 March 2018

Kalli Taswirar Sabuwar Gadar Da Gwamna Ganduje Zai Gina A Kano

 Wannan shine zanen sabuwar gada mai hawa uku d Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR zai gina a shataletalen Dangi dake kan titin zuwa Gidan Zoo, aikin zai hada da gadar kasa ga masu wuce wa ko dawo wa akan titin Zaria, sai kuma masu yin kwana a ko wanne sako a doron kasa, sannan sai gadar sama kuma wadda zata taso daga kan titin Gidan Zoo ta sauka a gefen Massallacin Aliu Ibn Abu Talib. 

Wannan aiki dai za a gina shi ne akan kudi naira bilyan 4 kuma ana sa ran fara shi daga wannan wata na Maris, sannan a kammala shi cikin wata goma In Sha Allah. 

Daga Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser New Media
Government House Kano

No comments:

Post a Comment