Thursday, 22 March 2018

Kalli yaron dake tura mahaifiyarshi zuwa gurin aiki akan keken guragu kullun kamin ya tafi makaranta: Idan ya dawo kuma yaje ya daukota

Wannan hoton wani yarone dan kasar Kenya dake yawo a shafukan sada zumunta, labarin yaron akwai birgewa da ban tausai, kamar yanda labarin yazo, yaron yakan tura mahaifiyarshi akan keken guragu kullun da safe zuwa gurin da take sana'a kamin daga nan ya wuce makaranta.Haka kuma idan ya dawo daga makaranta da yamma zai sake zuwa ya tura mahaifiyar tashi su tafi gida, yanayin rayuwarsu akwai ban tausai.

No comments:

Post a Comment