Monday, 12 March 2018

Karanta irin yanda ake yin Allah wadai gugar zana da Tir da rawar da Fatima Ganduje tayi

Bayan da hotunan bidiyon diyar gwamnan Kano, Fatima Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana tana ta tika rawa a gurin bikinta, da dama daga cikin mutane sunyi Allah wadai da hakan, kuma wasu sunyi sharhi akan wannan batu na rawar ta Fatima.Sanannen me fadakarwarnan a dandalin sada zumunta da muhawara na Twitter, watau Mustafa Angry Ustaza, duk da be fito ya kama suna ba yace" Ya Allah kar ka bamu arziki ko matsayi da zai sa mu rasa tarbiyya da koyin da Annabi(S. A. W) ya mana duk da sunan wayewa. Amin"
Shi kuwa me sharhi akan lamurran siyasa da al'amuran yau da kullun, Gimba Kakanda ya bayyana cewa, Watau Hisba tarbiyyar 'ya'yan talakawa kadai suke kulawa, yace yana inkarin irin salon shari'ar da masu fada aji na Arewa suka kawo mana, inda akaita sukar Rahama Sadau da kakkausar murya lokacin da tayi abinda be dace ba amma ga 'ya'yan 'yan siyasa ana ta karfafasu akan irin wannan abu na rashi tarbiyya. A karshe yace munafurci dodone...

Shi kuwa wani bawan Allah me suna Ahmad Muhammad cewa yayi, malamai kullun suna magana akan tarbiyyar yara gaba daya, da kuma badala da akeyi a bukukuwa basa bambance tsakanin dan me kudi da talaka, ya rage naka ka dinga sauraron karatuttukan ba dole se abinda ya watsu a Instagram ko Twitter ba.
Shima wani me suna Khalil cewa yayi, Malam, Tarbiyya tayi a rayuwa kaji. Allah ya sakawa iyayenmu da Alkhairi da gidan Aljannah.

No comments:

Post a Comment