Sunday, 18 March 2018

Karanta zazzafar amsar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya baiwa wani da ya tambayeshi suna ina akayi badala a bikin diyar Ganduje?

Bayan da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana daurin auren zawarawa dari da ya halarta a Argungu wanda gwamnatin jihar Kebbi tayi, kuma ya bayyana cewa anyi bikin auren babu badala babu fitsara, wani ya tambayeshi shin suna ina akayi badala a ranar auren diyar Ganduje?.Malam dai ya amsa mishi da cewa 'Mai yasa kuka kasa fito da zakzaky lokacin da burutai ya saka shi a shara?"
Duk da wannan bawan Allah tambayar da yayi ana ganin yayi fitsara amma wasu sunce da Malam din ya barshi be bashi amsa ba da yafi.

Daganan dai, wannan bawan Allah be sake cewa komaiba.

No comments:

Post a Comment