Tuesday, 13 March 2018

Karata dabarar da wannan bawan Allan yayi wajan sayar da abin sayarwarshi

Wani bawan Allah me suna Mohammed Ahmed Gorko ya bayar da labarin yanda yayi dabarar sayar da lemun Citta da yake talla a shekarar 2008, yace, a shekarar 2008 lokacin yana tallar lemun, sai ya kaiwa wani me shago ko zai siya, me shagon yace mai ya ajiye katan daya yaga ko zaiyi kasuwa.


Bayan ajiye lemun sai Mohammed ya samu abokanshi inda ya gayamusu da su zagaya su saye lemun a shagon mutumin, ai kuwa cikin kwana biyu lemun ya kare.

Me shago yaga lemu yayi kasuwa, ya kira Muhammad yace maza ya karo mai katan hamsin dan yaga lemun nashi yayi kasuwa.

No comments:

Post a Comment