Tuesday, 20 March 2018

Kasar China ta kwaikwayi birnin Paris

Ashe dai kasar Chaina ba kayan masarufi na yau da kullun kadai take kwaikwaya daga kasashe da Kamfanonin Duniya ba, hadda gari guda sukutum, Kasar Chinar ta kwaikwayi birnin Paris na kasar Faransa dake jan ra'ayin dubban masu yawan bude ido.


Kasar ta China ta gina sananniyar hasumiyarnan nan ta kasar Faransa da ake kira Eiffel Tower da kuma wasu karin guraren tarihi a wani karamin gari me suna Tiandecheng, wani me daukar hoto na kasar ta Faransa da ya ga hotuna kuma yaji labarin wannan gari da China ta kwaikwayi birnin na Paris ne yayi takakkiya har kasar ta China ya kuma je wannan gari dan ganewa idonshi abin mamaki.
Me daukar hoton yace babu banbaci tsakanin gine-ginen Faransar da wanda Chinar ta kwaikwaya, kawai sai dai sabuntaka dana Chinar suka fi na Faransa, hatta yawan filawoyin dake shuke a gaban gine-ginen na Faransa duk Chinar tayisu daidai babu kiskure.

Kawai banbancin shine yawan mutane da kuma al'adar mutanen garin.

Ya kara da cewa ba wai masu yawon bude idone kadai ke a wannan kirkirarren gari na China ba, akwai mutanen dake zaman dindindin kuma suna ayyyukansu na yau da kullun.
CNN/Daily Mail UK/

No comments:

Post a Comment