Tuesday, 6 March 2018

Ko 'yan hamayya za su yaba mana kan tsaro>>Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ko 'yan hamayya da masu tsananin kushe za su yi amince cewa gwamnatinsa ta yi kokari wajen inganta harkar tsaro a kasar, tun daga hare-haren Boko Haram.Shugaban ya fadi hakan ne a yayin da ya kai wata ziyarar jaje jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar, a jerin ziyarar da ya fara ranar Litinin zuwa jihohi biyar da ke fama da rikice-rikice ko dai na manoma da makiyaya ko na masu tayar da kayar baya.

Ya kara da cewa tun bayan hawansa mulkin kasar nan gwamnatinsa ke mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro.

Shugaba Buhari ya kuma jajantawa al'ummar jihar Taraba kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi sakamakon rikicin baya-bayan nan da ya faru tsakanin manoma da makiyaya.

A yayin ziyarar tasa a Taraba, Shugaba Buhari ya yi ganawa ta musamman da sarakunan gargajiya na jihar da shugabannin al'umma da wakilan makiyaya da manoma da manyan jami'an tsaro da kuma manyan jami'an gwamnatin jihar, inda ya ji ta bakinsu kan abubuwan da ke faruwa.

Ya ce kokarin da ake na samar da zaman lafiya yana bukatar cikakken goyon bayan sarakunan gargajiya, musamman wajen ganin sun roki al'ummarsu da su dinga girmama rayukan juna.

'"Na zo nan ne musamman don na gana da sarakunan gargajiya da kuma gwamnatin jiha, don na mika musu sakon ta'aziyyata tare da jajantawa wadanda suka rasa 'yan uwansu suka kuma yi asarar dukiya.

"Ina so ku san cewa gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta magance rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya, kuma za ta ci gaba da neman goyon bayan sarakunan gargajiya don sanin muhimmancinsu wajen kawo zaman lafiya a tsakanin al'umma, in ji shi.

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku wanda ya tarbi shugaban ya ce ya karbi shugabanci ne daga jihar da dama can ke fama da rikicin kabilanci, amma gwamnatinsa tare da hadin gwiwar jami'an tsrao na iya kokarinsu don ganin sun sasanta kungiyoyin da ke fada da juna.
Su kuwa sarakunan gargajiya cewa suka yi, kamata ya yi a samar da wata tsattsaurar doka da za a dinga hukunta duk wanda aka kama da hannu a tayar da zaune tsaye, don hakan ne kawai zai rage rikice-rikicen.

Shugaban kasar dai ya yi alkawarin tabbatar da hakan ta hanyar gurfanar da duk mai hannu a janyo rikici a gaban shari'a da kuma daukar mataki a kansu.

Shugaban yana ziyartar jihohin Taraba da Zamfara da Benue da Yobe da kuma Rivers ne.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment