Thursday, 29 March 2018

Kotu ta wanke mutumin da aka daure shekaru 45 a gidan yari bisa kuskure

Wani mutum dan kasar Amurka da aka daureshi tsawon shekaru arba'in da biyar bisa zargin kisan da be aikataba, kotu ta bayyana cewa mutumin da ya bayar da sheda akanshi ne yayi karya dan haka ya samu kotun ta wankeshi daga laifin, mutumin dan shekaru saba'in da  daya da ake kira Richard Philips ya bayyana cewa be cika saka abu a ranshi ya dameshi ba dan haka be sakawa kanshi damuwar shekarun da yayi a gidann yari bisa kuskure ba


Ya kara da cewa abu daya da yake burin yi shine gamuwa da 'ya'yanshi biyu wanda lokacin da aka daureshi shekarunsu 4 dayan kuma shekarunshi 2 kuma tun daga lokacin be kara jin duriyarsu ba.

Rahoton ya bayyana cewa Philip shine mutumin da ya fi dadewa a daure a gidan yari a kasar ta Amurka bisa laifin da be aikataba, kuma wata kila a biyashi kudin diyyar daurin da aka mishi bisa kuskure da suka kai dalar Amurka miliyan biyu.
CNBS.

No comments:

Post a Comment