Friday, 9 March 2018

Kuma dai: Mabiya addinin Buddah sun farwa musulmai a kasar Sirilanka

Rahotanni daga kasar Sirilanka na cewaabiya addinin Budda sun rufarwa dukiyar musulmai da tsirarune a kasar da kuna da kuma wawa, lamarin ya farune tun ranar Lahadin data gabata, inda hatsaniya ta hada wasu matasan musulmai da wani matashin buddah inda musulman suka mai dan karen duka har ya samu raunuka, kamar yanda The Hindu suka ruwaito.


Wannan ya harzuka matasan addinin Buddah inda suka farwa musulmai wanda dama tsirarune, da fasa shagunan da suke kasuwanci da kuma kona gidajensu.

Kamfanonin dillancin labaran Reuters da na AP sun ruwaito cewa rikicin ya kara kazancewane bayan da mabiya addinin Buddah suka zargi wasu musulmai da shiga gurin ibadarsu suka musu satar kudin da suke tarawa, wannan yasa mabiya addinin Buddahn suka kama kona gidaje da dukiyoyin musulmai babu kakkautawa.

Wasu daga cikin musulman sun shiga cikin wani katon masallaci dan neman mafaka kuma sun zargi jami'an yan sanda da hanasu kwashe dukiyoyinsu da kuma barin matasan addinin Buddah suna kona musu dukiyoyinsu da gangan.

Haka kuma koda a kwanakin baya wasu masu tsattsauran ra'ayi a kasar ta Sirilanka sunyi zanga-zangar kin amincewa da musulmai 'yan gudun hijira da suka shiga kasar daga kasar Myammar wanda acan ma mabiya addinin Buddahnne ke yiwa musulmai kisan kare dangi.

Kasar ta Sirilanka dai ta saka dokar hana fita a yankin da rikicin ke faruwa,.

Allah shi kyauta ya kuma kai musu dauki

No comments:

Post a Comment