Monday, 19 March 2018

'Kwankwaso be gana da Obasanjo ba'

Bangaren tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya karyata labarin cewa Kwankwason ya gana da Obasanjo a Legas kamar yanda ake ta yadawa, Daily Trust ta ruwaito cewa daya daga cikin na kusa da Kwankwason, Binta Spikin ta musanta labarin inda tace Kwankwaso yana Kaduna inda yake Ganawa da 'yan kwankwasiyya daban-daban da suka kawo mai ziyara daga Kano.


Haka kuma tsohon kwamishina a zamanin mulkin Kwankwason, Yunusa Dangwani ya bayyana cewa wanca labarin ba gaskiya bane, inda ya kara da cewa duk abinda zasuyi a matsayinsu na 'yan kwankwasiyya suna shaidawa 'yan jaridu basa yi a boye, suma wancan labari ji sukayi a jaridu da kuma kafafen sada zumunta na yanar gizo.

Wasu kafafe sun ruwaito cewa Sanata Kwankwason ya gana da Obasanjo wanda har yana tunanin tsayar dashi a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu, karkashin sabuwar hadakar da ya bude ta ceto 'yan Najeriya daga halin da suke ciki.

No comments:

Post a Comment