Saturday, 31 March 2018

Leah Sharibu tayi yunkurin kubucewa daga hannun 'yan Boko Haram

Daya daga cikin 'yan makarantar Dapchi da mayakan Boko Haram suka sace kuma suka dawo dasu amma ita suka rike ta saboda bata amshi addinin musulunci ba, Leah Sharibu tayi kokarin kubucewa daga hannun 'yan Boko Haram din.


Da ya daga cikin yaran da aka dawo dasu ne ta bayyana haka, kamar yanda shafin Cable ya bayyana, Sharibu da wasu 'yan matan sun samu suka gudu daga hannun 'yan Boko Haram inda suka yi tafiyar kwanaki a kasa amma sai suka fada hannun wasu mutane da suka mayar dasu gurin 'yan Boko Haram din.

Rahoton ya kara da cewa bayan da aka dawo dasu hannun 'yan Boko Haram din, sun yi dariya suka tambayesu cewa yanzu ku gurin kafirai zaku koma?

No comments:

Post a Comment