Friday, 2 March 2018

Magu be aikata laifin komai ba: Saboda haka ba za'a cireshi ba>>Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa baza'a cire shugaban hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ,Ibrahim Magu daga mukaminshi ba saboda babu wani laifi da ya aikata.


Kamar yanda jaridar Vanguard ta ruwaito, Osinbajo ya bayyanawa wasu zababbun kafafen watsa labaraine hakan a wata ganawa da yayi dasu a fadar shugaban kasa, ya kara da cewa yasan Magu tun lokacin tsohon shugaban hukumar, mutumin kirkine ba ruwanshi saboda haka ba za'a canja shiba tunda babu wani laifi daya aikata.

Majalisar dattijai dai taki amincewa da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC saboda bai cika sharuddansu ba kamar yanda sukace amma bangaren zartarwa yaki canja Magun har yanzu, hakan yasa majalisar ta nuna fushinta ta hanyar jingine tantance sauran wasu ayyuka da bangaren zartarwa ya aike mata.

No comments:

Post a Comment