Wednesday, 14 March 2018

Majalisa ta dage dakatarwar da akawa Abdulmumini Jibril

Majalisar wakilai ta dage dakatarwar data wa dan majalisa me wakiltar mazabar Kiru da Bebeji daga jihar Kano watau Abdulmumini Jibril, da yake bayani akan dage dakatarwar da akawa Jibril, kakakin majalisar wakilan yace ya rubuta musu wasikar bada hakuri kuma ya cika dukkan sharuddan da aka gindaya mishi saboda haka an dage dakatarwar da aka mishi zai iya dawowa aikinshi duk sanda yaso.


A shekarar 2017 ne dai majalisar ta dakatar da Abdulmumin Jibril na tsawon kwanaki dari da tamanin bayan da ya zargi cewa anyi cushe a cikin kasafin kudi, amma tsawon lokacin dakatarwar da aka mishi din ta wuce kwanaki dari da tamanin din, kadanne be cika shekara guda ba, kamar yanda Premium Times ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment