Wednesday, 21 March 2018

Majalisar Dattijai ta karrama Sanata Ali Wakili: Zamu kula da iyalanshi>>Inji Sanata Saraki

Majalisar dattijai ta karrama marigayi, Sanata Ali Wakili inda aka dora filawa da tutar Najeriya akan kujerar da yake zama sannan akayi shiru na 'yan mintuna dan girmamawa, a gareshi, Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa dukansu a majalisar suna girmama marigayin saboda mutumne me tsage gaskiya komi dacinta.Ya kara da cewa a lokacin da suka bashi shugabancin kwamitin rage radadin talauci, yaki karba amma daga baya sai ya amsa kuma ya bayar da gudummuwar da ake bukata, Saraki yace zasu ci gaba da mai addu'a da kuma kulawa da iyalinshi do min suma yanzu sun zama iyalanshi.

Allah ya jikan sanata Ali Wakili.

No comments:

Post a Comment