Thursday, 8 March 2018

Majalisar dattijai zata iya yin gaban kanta wajan kafa askarawan Peace Corps

Rashin sawa dokar da zata kafa hukumar askarawan Peace Corps Hannu da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ya dauko hankulan mutane sosai a kasarnan, shugaba Buharin ya bayar da dalilai na rashin kudi da kuma cewa ayyukan da Peace Corps din ke sonyi, 'yansanda da wasu sauran jami'an tsaro da ake dasu a kasarnan na yinsu.


To saidai sanata daga jihar Kogi watau Dino Melaye yace yana samun matsin lamba daga mazabarshi akan kafa asakarawan peace Corps din kuma yana mamakin ace wai babu kudin kafa wannan hukuma bayan gwamnatin APC ta ciwo bashin kudi tiriliyan goma sha daya, sama da bashin da PDP ta ciwo na tiriliyan shidda a tsawon shekaru sha shida da tayi tana mulki, yace me zai hana ayi amfani da wancan kudin wajan kafa wannan hukuma?.

Yayi kira ga shugaban kasa da ya sake dubar wannan shawara da ya yanke akan kafa askarawan na Peace Corps in ba haka ba majalisar dattijan tayi gaban kanta wajan kafa hukumar.

Dino Melaye dai yayi wannan jawabine a gaban majalisar lokacin da take zamanta a jiya, amma shugaban majalisar bece komai akai ba kuma babu wani dan majalisar da ya nuna goyon baya ko kuma kushe ga wannan jawabi na Dino Melaye.
Vanguard

No comments:

Post a Comment