Sunday, 18 March 2018

Majalisar dinkin Duniya ta baiwa A'isha Buhari jakadanci

Bangaren majalisar dinkin Duniya dake kula da yaduwar cutar kanjamau ya nada uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari a matsayin jakadiyar su, kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito cewa an baiwa A'isha wannan jakadancinne saboda irin yanda take nuna damuwa da halin da al-umma musamman yara da mata da matasa marasa galihu suke ciki.


Wannan jakadancin zai bata damar kula da raguwar yaduwar cutar ta kanjamau tsakanin uwa me dauke da ita da kuma dan da zata haifa da kuma kula da ganin cewa ana yiwa mata masu dauke da ciki gwajin cutar kamin lokacin haihuwarsu.

Muna tayata murna.

No comments:

Post a Comment