Tuesday, 27 March 2018

Majalisar dinkin Duniya tayi kira ga Najeriya ta halatta amfani da tabar wiwi

A wani taro da majalisar tarayya ta shirya dan gano hanyar magance amfani da magunguna da wasu matasa keyi wajan mayar dasu kwaya suna bugar dasu,wakiliyar majalisar dinkin Duniya ta yi kira ga Najieriya da su halatta amfani da tabar wiwi.


Wakilaiyar tace, majalisar dinkin Duniya ta halatta noma da kuma amfani da tabar wajan samar da magani dan haka take kira ga Najeriya da itama tabi sahu dan amfanin al-ummarta.

Saidai wakiliyar ta kara da cewa ya kamata hukumomi su kara saka ido wajan hana fasa kwaurin magunguna da kuma hana amfani dasu ta hanyoyin da basu dace ba.

No comments:

Post a Comment