Thursday, 8 March 2018

Majalisar Sanatoci taki amincewa da kudirin dokar da zai baiwa matasa masu bautar kasa damar canja kayan bautar kasar yanda zai dace da addini da al'adarsu

Majalisar Dattijai ta kasa taki amincewa da kudirin dokar da zai baiwa matasa masu bautar kasa canja kayan bautar kasar yanda zai dace da addini da al'adarsu, Sanata Emmanuel Bwacha daga jihar Tarabane ya gabatar da kudirin a gaban majalisar inda ya bayyana cewa ya samu korafe-korafe daga mutane da dama akan wando da ake amfani dashi a kayan bautar kasar wanda dalilin haka wasu mata da dama sun hakura da bautar kasar saboda addininsu ko al'ada bata dace da saka wando ba.


Dan haka yake kira da a saka cikin doka cewa matasan masu bautar kasa zasu iya canja kayan bautar kasar zuwa yanayin da zai dace da addini da al'adarsu.

Sanata Abubakar Kyari daga jihar Borno da sanata Barau Jibrin daga jihar Kano sun goyi bayan wannan kudiri amma daga karshe da akayi kuri'a tsakanin sanatocin be samu karbuwa a majalisarba.

Wasu daga cikin dalilan da sanatocin da suka ki amincewa da wannan kudiri suka bayar sun hada da cewa, saka wannan batu cikin doka yana bukatar canja dokar da ta kafa Hukumar bautar kasar wanda hakan zai dauki dogon lokaci sannan kuma ita kanta hukumar ta bautar kasar tana da hurumin canja wadannan kaya ba tare da sa hannun majalisa ba, haka kuma ba Sanata bane ya kamata ya kawo wannan kudiri ba, shuwagabannin addinan da wannan abu ya shafa ya kamata ace sun matsawa hukumar ta bautar kasa watau NYSC ta canja wadannan kaya.

Saidai shima Sanata Bwacha ya soki sauran Sanatocin akan kin amincewa da wannan kudiri inda ya bayyananawa manema labarai cewa ansa son rai wajan kin amincewa da kudirin.

No comments:

Post a Comment