Friday, 9 March 2018

Makarantun kudi na tsaka me wuya a jihar Kaduna: Duk malamansu sun koma aiki da makarantun gwamnati>>Gwamna El-Rufai

A kokarin da yake na gyaran ilimi a jihar Kaduna, Gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa makarantun kudi a jihar suna cikin tsaka me wuya domin kuwa duk malansu sun koma suna neman aiki a karkashin sabon tsarin gwamnatin jihar na daukar ingantattun malamai dan habbaka ilimi a makarantun gwamnati.


Gwamnan ya kara da cewa yana fatan nan da shekaru biyar masu zuwa makarantun kudi a jihar ta Kaduna zasu zama saidai kawai mutum yakai danshi dan yana so amma ba dan ba'a bayar da ingantaccen ilimi a makarantun gwamnatiba.

No comments:

Post a Comment