Saturday, 3 March 2018

Manyan baki sun hallara a garin Kano dan halartar daurin auren 'ya'yan gwamnonin Kano da na Oyo


Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR tare da sirikin sa Mai Girma Abiola Ajimobi Gwamnan Jihar Oyo wanda zaa daura auren yayan su a yau, Fatima Abdullahi Umar Ganduje da Abolaji Ajimobi.
A tare da su akwai Sakataren Gwamnatin Taraiya Boss Mustapha da Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari da na Kogi Alhaji Yahaya Bello da Ministan cikin gida  Alhaji Abdurrahman Dambazau da Gwamnan Jihar Maradi daga Kasar Nijar Alhaji Zakari Umaru da  Mataimakin Gwamnan Ondo Mr Agbola Ajayi da Alhaji Abdussamad Isiaku Rabiu da sauran manyan baki, inda suke shirye shiryen taran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari an jima kadan.

Salihu Tanko Yakasai

No comments:

Post a Comment