Sunday, 25 March 2018

Manyan kifaye 150 sun mutu a gabar ruwan kasar Australia

Wasu manya-manyan kifaye sun bayyana a gabar ruwa a kasar Australia da yawan su yakai dari da hamsin duk a mace in banda guda goma sha biyar da ga cikinsu, lamarin ya dauki hankulan mutane inda ma'aikatan agaji da likitocin dabbobi suka kawowa kifayen dauki.


A karshe dai guda shida ne kawai daga cikin kifayen suka rayu, aka mayar dasu cikin ruwan amma sauran duk saidai kwashe su akayi.

Wannan lamari dai ba kasafai ya cika faruwa ba a Duniya, kamar yanda kafofin labarai na Reuters, Guardian/Uk da Buzzfeed suka ruwaito, rabon da a ga kifaye da yawa haka a gabar ruwa a mace tun shekaru ashirin da biyu da suka gabata.

Andai killace gabar ruwan inda aka hana mutane shiga dan a kwashe kifayen.

No comments:

Post a Comment