Tuesday, 20 March 2018

Manyan kungiyoyi na shinshinar Mohammed Salah akan kudin da suka fi wanda aka sayar da Neymar

Rahotanni daga jaridar the sun suna nuna cewa manyan kungiyoyin kwallon kafa uku, Real Madrid da Barcelona da PSG suna shinshinar tauraron dan kwallon Liverpool, Muhammed Salah akan kudin da sukafi  wanda aka sayi Neymar.


Tauraruwar Muhammed Salah tana haskakawa sosai a Liverpool inda yake cin kwallaye babu kakkautawa abinda har yakai aka fara hadashi da Messi, saidai Liverpool ta bayyana cewa bata da niyyar sayar da Salah din a yanzu.

Amma wasu na ganin wannan ma shine zai sa dan wasan ya kara tsada sosai.

No comments:

Post a Comment