Sunday, 25 March 2018

Maryam Booth ma ta yiwa masu amfani da sunanta suna bata mata suna a shafukan yanar gizo Allah ya isa

Itama tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth ta bi sahun abokiyar aikinta, Rahama Sadau inda tayi Allah ya isa ga masu amfani da sunanta a shafukan sada zumunta suna bata mata suna, Maryam tace ita ta taso gidan tarbiyya kuma tasan mutuncin dan Adam.


A karshe ta bayyana cewa Allah ya isa abinda suka mata ba zata yafe ba Duniya da lahira.

Ta kuma bayyana dandalinta na Facebook na ainihi.

A makon daya gabatane dai shafin hutudole.com ya wallafa labarin Maryam inda ta soki Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da cewa Munafurcine ya hanashi yin magana akan diyar gwamnan Kano da tayi raye-raye da hotunan badala a bikinta, labarin da ya watsu kamar wutar daji.No comments:

Post a Comment