Tuesday, 13 March 2018

Maryam Booth na nemawa wani gwanin iya zane tallafi

Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth na nemawa wannan bawan Allah da suke tsaye tare a wannan hoton na sama taimako gurin mutane, tace sunanshi Ahmad, yana da shekaru hamsin da biyu a Duniya kuma Allah ya bashi basirar iya zane ta yanda cikin mintuna biyar zai iya zana duk wani abu daya gani, amma a titi yake kwana saboda talauci.


Dan haka Maryam take rokon masoyanta dasu taimakawa wannan bawan Allah da koda nera dari-darine domin tallafawa rayuwarshi da ta iyalanshi tace duk wanda yake son bayar da taimakon sai ya tuntubeta.

No comments:

Post a Comment