Monday, 12 March 2018

Maryam Sanda da ake zargi da kashe mijinta: 'Bata shiryawa diyarta bikin zagayowar ranar haihuwarta ba'

Wani rahoto ya karyata labaran da aka watsa na cewa matar da ake zargin ta Kashe mijinta, Maryam Sanda wai ta shiryawa diyarta bikin ranar zagayowar ranar haihuwara kwanaki biyu kacal da bayar da belinta daga gidan yari.


Jaridar Leadership ta bayyana cewa wancan labarin ba haka yake ba, domin iyalan Maryam sun fito sun karyata shi, kuma sun zargi wasu kafafen labarai musamman na yanar gizo da rashin yi musu adalci, sunce babu wata kafa da ta samu wannan labari ta tuntubesu taji ko gaskiyane ko kuwa akasin haka amma saidai kawai aka yita watsashi.

Ainihin abinda ya faru shine, dama can tun kamin lamarin kisan Bilyaminu, iyalan gidansu sun dauki al'adar yiwa diyar ta Maryam, shagali da daukar hotuna duk lokacin da ta cika wata daya da haihuwa, to saboda abinda ya faru, basu samu aka ci gaba da waccan al'adaba, kuma yanzu gashi ta cika shekara daya da haihuwa, shine kakarta ta kira me daukar hoto ya dauke ta hotuna dan a ajiye mata tarihin ranar da ta cika shekara daya a Duniya.

Sun kara da cewa wane irin bikin zagayowar ranar haihuwane za'ayi wanda zaka ga babu yara, babu wani da aka gayyata?, idan aka lura da hotunan yarinyar, ita kadaice a cikin hotunan sai balambalam da aka sa mata. Kuma hoton da aka hada wanda Maryam ke rike da ita, tsohon hotone wanda tun yarinyar tana da watanni biyar aka daukeshi. Asalima lokacin da aka dauki wadannan sabbin hotunan ita Maryam tana can gadon asibiti a kwance.

Sun kara da cewa 'yar uwar mahaifin yarinyar kadai aka aikawa da hotunan acan jihar Kebbi, kuma sunyi mamakin ganin hotunan sun shiga Duniya, inda saboda son rai da son bata suna aka saidawa 'yan jarida hotunan da kuma basu labarin karya akai suka yada.

Sun kara da cewa sun fahimci mutane na son ayi adalci a kan wannan abu da ya faru suma kuma suna so ayi adalci dan haka kamata yayi a bari aga hukuncin da alkali zai yanke tundadai ita Maryam na fuskantar shari'a.

No comments:

Post a Comment