Thursday, 29 March 2018

Me wankin mota ya sayar da motar da aka bashi wanki, yayi aure da kudin

Wani me aikin wankin mota a babban birnin tarayya, Abuja, Muhammad Chado ya tsere da wata mota da aka bashi ya wanke kirar Toyota Camry inda a karshe ya sayar da ita akan kudi dubu dari hudu da hamsin sannan yayi aure da kudin.


Hukumar 'yan sanda na Abujane suka kamo Chado kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito, bayan da ya sace motar ya koma kauyensu dake can jihar Naija inda ya buya, amma da yake dubu ta cika saida hukuma suka zakuloshi.

Choda ya shaidawa manema labari cewa ya sayar da motar akan kudi naira dubu dari hudu da hamsin, yayi amfani da dubu dari uku yayi aure sannan ya sayi kayan abinci da sauran kudin. Yanzu dai yana hannun hukuma.

No comments:

Post a Comment