Saturday, 3 March 2018

Miliyan biyar matashin da aka kama yana amfani da sunan sarkin Kano a Instagram yace in bashi>>Inji Mawaki Paul Okoye


Lallai masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce kowa ya debo da zafi, bakinsa, tauraron mawakin turanci, Paul Okoye ya bayyana irin damfarar da matashinnan da aka kama yana amfani da sunan sarkin Kano a shafin Instagram yana yaudarar mutane.


Paul ya bayyana cewa matashin ya taba zo mishi da bukatar ya bashi kudi har naira miliyan biyar kuma ya amince har ma ya baiwa matshin lambar wayarshi duk a tunaninshi da sarkin Kano yake magana. Amma yace muryar matshin da yaji ce yasa ya fara tunanin aya kuwa wannan sarkin Kano ne, kuma ta yaya wanda ya taba zama gwamnan babban bankin Najeriya zai tambayeshi kudi?

A wani sako da hotuna da Pauldin ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta da muhawara na Instagram za'a iya ganin wani bangare na tattaunawar da sukayi a asirce.

Abinda dai ya rika daukar hankalin mutane har suka rika sakin jiki da wannan matashi shine ganin cewa shafin na Instagram ya tantance dandalin da yake amfani dashi a matsayin sarkin Kano.

To sai muce Allah shi kyauta, yasa mu fi karfin zuciyarmu.

No comments:

Post a Comment