Thursday, 1 March 2018

Ministan cikin gida ya baiwa shugaban 'yansanda na kasa umarnin komawa Arewa maso gabas da zama

A kokarin da gwamnati take yi na samar da tsaro a yankunan Arewa maso gabas, musamman dalilin satar yaran makarantar Dapchi, ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya baiwa shugaban 'yan sanda, Ibrahim Idris da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, Abdullahi Muhammadu Gana umarnin komawa yankin Arewa maso gabas da zama dan su tabbata an kai jami'an tsaro makarantu a yankunan dake fama da tashin tashinar Boko Haram na jihohin Borno, Yobe da Adamawa.


Sanarwar tace shuwagabannin biyu zasu hada kai da kwamandan rundunar soji ta Lafiya Dole dake Maiduguri dan gudanar da wannan aiki nasu. Wannan sanarwar na zuwane bayan da a ziyarar da ya kai jihar Yoben tare da tawagar wakilan gwamnatin tarayya, Dambazau ya baiwa kwamishinan 'yan sanda na jihar umarnin saka jami'an na 'yansanda a makarantun dake yan kunan dan kare yara dalibai daga harin miyagu.


No comments:

Post a Comment