Thursday, 22 March 2018

'Mu ba 'yan Boko Haram bane: Ba mu da hurumin kama diyar gwamna>>Sheikh Daurawa

Shugaban hukumar Hisba ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yayi karin bayani akan rashin daukar matakin da hukumar Hisbar bata yi ba akan diyar gwamnan jihar Kanon, Fatima Abdullahi Ganduje saboda rawa da kuma hotunan da sukayi ita da mijinta a lokacin bikinsu da suka jawo cece-kuce.


Da yake tun farko dai Malam ya bayyana cewa baya Kano lokacin da abin ya faru inda har ya tambayi masu sukar tashi da cewa me suke so yace. Ya kuma yi karin bayani a masallacin Ansarussunnah dake Fage a Kano, inda yace lokacin da abin ya faru mutanen gari nata so suji me zaice amma malaminshi wanda yana ganin kimarshi yace mai kada yayi magana saboda haka ya samu kanshi cikin tsaka mai wuya.

Idan beyi magana ba jau, idan kuma yayi ya sabawa malaminshi, wannan dalilin yasa yayi shiru kuma ya kauracewa ofishin Hisbah din saboda 'yan jarida da sukayi dafifi suna jiranshi su mai tambayoyi akan rashin daukar matakin da Hisbar batayi ba akan diyar gwamnan.

Malan ya kara da cewa akwai abubuwa da dama da yayi duk da cewa yana cikin gwamnati, misali a lokacin da akaso a gina gurin yin fim a jihar ta Kano ya tashi haikan ya soki wancan lamari kuma har daga fadar shugaban kasa an kirashi amma ya tsaya kai da fata akan ra'ayinshi haka kuma yanzu kungiyar kiristoci ta Najeriya ta dauki hayar lauyoyi goma sun kaishi kotu akan yaki da bijirewa dokokin addini da yake yi a tsakanin al-umma.

Ya kara da cewa basu da hurumin kama diyar gwamna domin su ba Boko Haram bane, ba zasu yi fada da gwambati ba, sojoji da 'yan sanda da jami'an farin kaya ke tsaron gurin bikin, 'yan Hisba ba zasu iya yin fada ko kuma ture wadannan jami'an tsaro ba dan su kama diyar gwamna ba.

Haka kuma ya kara da cewa Hukumar Hizba ta gwamnatice, dokar daya kafata ba ta bata karfin yin irin wancan kame ba, kuma akwai gurare da dama wanda idan sunje suka ga jami'an soji sukan kyale su barwa Allah tunda ba zasu yi fada dasu ba. Dan haka Malam ya tambayi masu sukarshi akan wannan lamari ya suke so yayi?, kamar yanda Daily Nigerian ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment