Friday, 30 March 2018

Musulma ta farko me saka Hijabi zata zama sarauniyar kyau a kasar Ingila

Musulma 'yar kaaar Ingila me suna Maria Mahmood na kan hanyar zama sarauniyar kyau ta kasar Ingilar ta farko dake sanya hijabi, Maria dai ta wuce mataki na biyu na tantancewa a gasar kamar yansa jaridar Mirror ta kasar Ingilar ta ruwaito kuma itace musulma ta farko me sanya hijabi da ta taba shiga gasar.


A shekarun baya akwai musulmar da ta taba zama sarauniyar kyau ta kasar Ingilar amma bata sanya Hijabi, Maria ta bayyana cewa iyayenta da abokanta da kungiyoyin addinin musuluncine suka dauki nauyinta kuma tana kokarin zama sarauniyar kyan kasar ta Ingilane dan ta kawar da irin kallon da akewa musulmai na cewa sunfi kwarewa a harkar ta'addanci da kuma ta kara karfafawa 'yan mata Musulami gwiwa akan cimma burinsu na rayuwa.

Tace duk da yake akwai masu ra'ayin 'yan mazan jiya dake sukar wannan abu da takeyi amma masu yabonta sunfi yawa dan haka zata cigaba.

A yanzu dai za'a ci gaba da wannan gasa ta sarauniyar kyau ta kasar Ingilar wadda mataki na gaba shine sanya rigar mama da pant kawai da 'yan mayan zasuyi dan aci gaba da tantancesu, amma Maria, 'yar shekaru ashirin tace ita ba zata saka irin wadancan kaya ba dan sun sabawa koyarwar addininta, zata ci gaba da saka hijabi da kayan mutunci.

Idan dai Maria taci gasar ta sarauniyar kyau ta kasar Ingilar itace zata wakilci kasar a gasar sarauniyar kyau ta Duniya, muna mata fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment