Wednesday, 28 March 2018

Mutane miliyan 20 na neman gurbin aiki dubu 100 a kasar Indiya

Hukumar jirgin kasa ta kasar Indiya zata dauki ma'aikata kimanin dubu dari daya amma yawan mutanen da suka aika da takardar neman aiki sun kai kimanin miliyan ashirin, kamar yanda kafar labarai ta BBC ta ruwaito, kasar Indiya na daya daga cikin kasashen Duniya da suka fi amfani da jirgin kasa wajan harkar sufuri.


Wannan labari ya dauki hankulan mutane sosai sannan kuma ya kara fito fili da irin yawan marasa aikinyi da kasar ta Indiya keda su, wani karin labarin yace akwai wanda ma irin takardun da suke dasu sun girmin aikin, akwai hadda masu digirin Phd dake neman aikin na kula da jirgin kasar.

Miliyoyin mutanene ke amfani da jirgin kasa a wajan tafiye-tafiyensu a kasar ta Indiya Kullun rana ta Allah.

No comments:

Post a Comment