Saturday, 3 March 2018

Na goyi bayan shugaba Buhari akan kada a kirkiro jami'an Peace Corps: Inganta aikin jami'an tsaron da muke da su yansu yafi kirkiro sabbi>>Dr. Tukur Adam Al-Manar

A satin daya gabatane shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kin amincewarshi ta sakawa dokar da zata kafa askarawan Peace Corps hannu, lamarin da ya jawo ra'ayoyin jama'a da yawa a kasarnan wasu suka yi na'am da wannan shawara ta shugaban kasa, wasu kuma suka soketa, malamin addinin musulunci, Dr. Tukur Adam Al-Manar ya bayyana ra'ayinshi, ko kuma shawara, kamar yanda ya bayyana akan wannan lamari.


Ya fara da cewa , Shawara ta akan kafa hukumar Peace Corps, Akwai jami'an tsaro da yawa a kasarnan, kalmar Peace Corps, watau jami'an ko kuma askarawan zaman lafiya, za'a iya amfani da ita akan jami'an Sojoji da 'yan sanda ko kuma jami'an civil defence, shin wadannan jami'ai ba an kafasu bane domin kare muradun kasarnan da tabbatar da zaman lafiya a kasarnan?. Shin ukunnan basu isa ba haka?, shin ana biyansu albashi me kyau, suna da isassun kayan aiki na zamani?, suna da kyawawan guraren zama? Suna da makarantu masu kyau da suke kai 'ya'yansu?, to dan me kuwa za'a bukaci Peace Corps yanzu?, me zai hana gwamnati ta dauki karin yawan wadannan jami'ai da muke dasu ta inganta albashinsu da basu kayan aiki na zamani domin magance matsalolin tsaro da muke fama dasu a kasarnan mai makon kirkiro Peace Corps, gwamnati ta kula da jami'an tsaron da muke da su a yanzu  yafi kirkiro sabbi, yawan makamai a hannun mutane da yawa bashi da amfani, ace 'yan sanda da bindiga, kwastam da bindiga, soja da bindiga kuma ace a sake kirkiro wasu, abin sai yayi yawa.

Wasalam.

No comments:

Post a Comment