Friday, 2 March 2018

Naira Miliyan uku me amfani da sunan sarkin Kano a Instagram ya damfari mutane

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II
'Yan sandan Jihar Kano sun ce mutumin da ke karyar cewa shi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ne a shafin Instagram ya damfari mutane da dama.'Yan sanda sun ce mutumin mai suna Sultan Bello matashi ne dan kimanin shekaru 20, kuma ya shaida masu cewa ya damfari mutane da dama.


DSP Musa Magaji kakakin rundunar 'yan jihar Kano ya shaidawa BBC cewa bincikensu ya gano ya damfari mutane kudi da suka kai akalla Naira miliyan uku.
'Yan sandan sun ce sun samu korafi daga wata da ta yi zargin cewa ya damfare ta kan wata waka da ta yi wa Mai Martaba Sarkin Kano.
'Yan sandan sun ce yana ba su hadin kai a binciken da suke gudanarwa kan irin yawan mutanen da ya zambata.
Matashin dai yana da mabiya fiye da 200,000 a Instagram da sunan Sarki Sanusi.
Kuma har ya samu damar da kamfanin Instagram ya tantance shi ta hanyar ba shi shudiyar alama.
Shafin dai ya kasance na sirri ne da sai an amince kafin ka fara bin sa duk da cewa yana da alamar tantancewar.
Kakakin 'Yan sandan Kano ya ce suna ci gaba da bincike, kuma za su tuhumi mutumin nan ba da jimawa ba da laifin yin sojan gona da kuma zamba.
Ya kara da cewa Sarkin na daga cikin mutum bakwai da aka yi sojan gona da sunansu, da suka hada da wasu manyan 'yan kasuwa da manyan masu fada a ji.
'Yan sanda sun ce mutumin da ake tuhumar ya samu mabiya a kalla miliyan uku a dukkan shafukan bogin da ya bude na kafafen sada zumunta.
Bai fadi dalilin da ya sa yake shigar sojan-gonar ba, amma bude shafuka mai dumbin mabiya irin haka na iya zama hanyar samun kudi ta hanyar samun tallace-tallace.
Kamfanin Instagram dai ya ce shafukan manyan mutane kawai yake sanyawa alamar shudi na tantancewa saboda gudun yi musu sojan-gona.
Shafin intanet din kamfanin ya ce: "Muna so mu tabbatar da cewa mutanen da ke amfani da Instagram za su iya saurin gane ko wadanda suke bi na gaskiya ne ba sojan-gona ba."

No comments:

Post a Comment