Saturday, 31 March 2018

'Najeriya ba zata koma kamar Somalia ba'>>Fadar shugaban kasa ta mayarwa da T. Y Danjuma martani

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta hannin me magana da yawunshi, Malam Garba Shehu yayi kira ga tsaffin shuwagabbin kasarnan da masu fada aji da su san irin kalaman da zasu rika furtawa mabiyansu musamman ganin irin yanda ake fama da matsalar tsaro a yanzu.


Shugaba Buhari ya bayyana cewa abin takaicine jin yanda wani me fada aji yake kira ga mutane da su dauki makamai dan su kare kansu, ya kara da cewa Najeriya hadin kai take bukata yanzu ba rikiciba, kuma za'ayi dukkan me yiyuwa dan hana Najeriya zama irin kasar Somalia.

Shugaba Buhari ya kuma yabawa jami'an soji bisa kokarin da suke na tabbatar da zaman lafiya a kasarnan.

A makon da ya gabatane dai aka ruwaito tsohon ministan tsaro, T. Y Danjuma yana kira ga mutanen Najeriya da su tashi su kare kansu daga masu kaimusu hari inda yace jami'an soji na goyawa masu kaiwa mutane hari baya.

No comments:

Post a Comment