Monday, 26 March 2018

'Nasha wuya a shekarun baya: Da kyar nike samun kudin siyan garin kwaki>>Inji me daukar hoton shugaban kasa

Tauraron me daukar hoton shugaban kasa, Bayo Omoboriowo ya bayar da labarin yanda rayuwarshi ta kasance a baya kamin ya zama me daukar hoton shugaban kasa, yace yasha wuya sosai, musamman lokacin yana makaranta, kudin da yake samu dubu biyune a wata, da kyar yake samun kudin siyan garin kwaki, wani lokacin ma harkuka yake yi.


Yace amma yanzu saidai idan ya tuna yayi murmushi saboda ya wuce gurin kuma duk da irin rayuwar da yake yi a wancan lokacin bata sa ya bar hankoron cimma burinshi ba, yau saidai kawai ya godewa Allah dan ya mishi komai.

Ya kuma karfafawa sauran, musamman matasa da cewa kada suyi kasa a gwiwa akan duk wani abu me kyau da suke sonyi, su jajirce da ikon Allah zasu sameshi.

No comments:

Post a Comment