Tuesday, 13 March 2018

Neymar na neman barin PSG ruwa a jallo

Tauraron dan wasan kwallon kafan kasar Brazil dake bugawa kungiyar PSG, Neymar na neman hanyar barin kungiyar ta PSG ruwa a jallo, tun bayan da Real Madrid ta fitar da PSG din daga gasar cin kodin zakarun turai Neymar yake ta kai gwauro yana kai mari wajan ganin yabar kungiyar ko ta halin kaka, yanzu dai Neymar din ya aikawa Cristiano Ronaldo da wasika akan wannan lamari.


Neymar din ya baiwa Marcelo takardar ne inda ya bukaci ya mikawa Ronaldo dan ya taimakamai wajan ganin ya dawo kungiyar ta Real Madrid, dama dai tuni me kungiyar ta Madrid Florentina Perez ya nuna bukatarshi ta sayan Neymardin.

To saidai rahotanni na nuna cewa ita kungiyar ta PSG bata da niyyar sayar da Neymar din a halin yanzu, amma wasu rahotannin sun bayyana cewa idan Brazil ta samu nasarar cin kofin Duniya Neymar din zai iya hakura ya zauna a PSG din.

Burin Neyamr dai na komawa Real Madrid shine ya gaji Ronaldo idan yayi riyata. Hakama rahotanni sun nuna Neymardin ya nemi komawa tsohuwar kungiyarshi ta Barcelona amma babu tabbacin zasu sake amsarshi.

Idan dai PSG din zata sayar da Neymar, ana kishin kishin din cewa zata sayar dashi akan zunzurutun kudi yuro miliyan dari hudu, watau kusan linkin kudin da suka siyoshi daga Barcelona.
Express Uk.

No comments:

Post a Comment