Monday, 19 March 2018

Neymar ya bukaci karin Albashi gurin PSG idan suna so kar ya canja kungiya

Tauraron dan kwallon kafa dake bugawa kungiyar PSG wasa, Neymar ya bukaci amai karin albashi idandai kungiyar ta PSG tana so yaci gaba da zama, kada ya koma wata kungiya, jaridar The Times  ta ruwaito cewa Neymar ya bukaci amai karin albashi na Yuro miliyan daya duk sati kamar yanda ya shaidawa me kungiyar ta PSG Nasser a lokacin da ya ziyarceshi a Brazil.


Haka ma akwai raderadin me kungiyar Real Madrid, Florentino Perez ya gana da dan wasan, Real Madrid dai na son sayan dan wasan a matsayin wanda zai maye gurbin Cristiano Ronaldo idan yayi ritaya, amma da alama Neymar kudi yake nema.

No comments:

Post a Comment