Tuesday, 13 March 2018

Nigeria za ta kara haraji a kan sigari da barasa

Ministar kudi ta Najeriya Mrs. Kemi Adeosun ta ce za a kara haraji a kan sigari da barasa.
Mrs Adeosun ta ce sabon matsayin gwamnatin zai samar da karin kudin shiga da rage matsalolin kiwon lafiya da ababen ke haddasawa.


Ministar ta ce Najeriya ta yi hakan ne domin aiwatar da umarnin kungiyar kawancen tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ta ECOWAS ko CEDAEO wadda ta bukaci mabobinta da su daidaita dokokinsu na haraji.

Mrs Kemi Adeosun wadda ta sanar da karin harajin a kan taba sigari da barasa da kuma dangoginta ta ce shugaba Muhammadu Buhari ne ya amince da karin.

Haka kuma gwamnati ta ware watanni uku masu zuwa domin daga kafa ga kamfanonin da ke samar da kayyakin a kasar.

Ministar ta kara da cewa baya ga kashi 20 cikin dari da gwamnati ke karba daga hannun masu sayar da taba sigari a kasar, daga ranar 4 ga watan Yunin wannan shekarar, gwamnati za ta kara harajin Naira daya a kan kowane karan sigari.

Ta kuma ce a badi za ta rubanya harajin zuwa Naira biyu, yayin da a shekarar 2020 za ta yi wani kari na kusan naira uku.

A jimillance dai gwamnati za ta kara harajin kusan naira shida a kan kowane karan sigari a cikin shekaru uku.

Haraji kan kaya masu sa maye

A bangaren giya kuwa, Mrs Adeosun ta ce gwamnati za ta yi karin harajin kwabo talatin a kan kowane sentilita, sannan za ta kara kwabo talatin da biyar-biyar a shekaru biyu masu zuwa, inda daga shekarar 2020 ne kuma harajin zai haura zuwa naira daya a kan kowace sentilita.

Hakazalika, gwamnatin za ta yi karin fiye da Naira biyar a kan kowane sentilita na wasu dangogin barasa a cikin shekaru uku.

Ministar ta kuma bayyana cewa karin harajin bai shafi sauran kayayyaki ba, kuma karin da ta yi a kan sigari da barasa ta yi shi ne don bin umarnin da kungiyar ECOWAS ko Cedaeo ta bayar cewa kasashen da ke karkashinta su daidaita dokokinsu na haraji da suka shafi wasu kayayyakin da ba na danyen mai ne ba.

Ministar kudin ta ce karin harajin zai zamo tamkar jifar tsuntsu biyu da dutse daya ne ga kasar, inda ake sa ran zai kara samar da kudaden shiga ga gwamnatin tarayya.

A daya bangaren kuma ana fatan zai rage matsaloli na lafiya da tabar da kuma giyar ke haddasawa ga masu tu'ammali da su. Sai dai ba ta yi wani karin haske ba kan yawan harajin da kasar ke sa ran samu ta wannan hanyar.

A shekarar 2012 Ostreliyata zamo kasa ta farko a duniya, da ta fito da wata dokar da ta sanya dole kamfanonin taba sigari ke yin kwali mara kayatarwa dake dauke da bayanan irin cututtukan da sigari ke haddasawa.

Sannan kasar za ta dinga kara haraji a kan sigarin, har sai an sayar da kwali daya a kan kimanin fam 24 wato kusan Naira 12,000 a kudin Najeriya.

Burtaniya ma ta bi sahun Ostreliya, inda a watan Mayun da ya gabata ne ta fara aiki da dokar yin kwalin sigari mara kayatarwa. Mashaya barasa na biyan haraji mai yawa a wadannan kasashe da ma wasu kasashe na duniya.
bbchausa.


No comments:

Post a Comment