Monday, 5 March 2018

Obasanjo ya cika shekaru 81: PDP sun bayyanashi a matsayin shugaban da babu irinshi

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya cika shekaru tamanin da daya da haihuwa, a sakon da suka aikamai na taya murna, jam'iyyar PDP sun bayyanashi a matsayin shugaba me hazaka wanda babu kamarshi a Najeriya.


Sunce yayi amfani da irin tsare-tsaren jam'iyyarsu ta PDP masu kyau lokacin yana mulki ya kawo abubuwan cigaba da dama a kasarnan.

Muna tayshi murna.

No comments:

Post a Comment