Friday, 30 March 2018

'Paparoma bece babu wuta ba'>>inji fadar Vatican

Fadar Vatican ta musanta labarin da dan jaridar kasar Italiya ya wallafa dake cewa Paparoma Francis yace wai babu wuta sai Aljanna kawai, sunce dan jaridar be fahimci Pop din bane kuma yamai fassarar da bata dace ba.


Sunce tabbas akwai wuta wadda Allah dai kona masu laifi.

A jiyane dai labarin na Pop ya watsu kamar wutar daji bayan da aka ruwaitoshi yace babu wuta wai masu zunubi kawai zasu bi iskane.

Jaridar Fox ta ruwaito cewa matsalar shi dan jaridar daya wallafa labarin baya nadar sautin murya a matsayin shaida idan yana hira da mutum shiyasa watakila ba za'a iya tantance labarin da ya wallafa ba.

No comments:

Post a Comment