Tuesday, 13 March 2018

Rahama Sadau ta zargi jakadan Najeriya a kasar Turkiyya da hana sarkin Kano kaiwa dalibai ziyara a kasar Cyprus

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau karkashin daliban dake karatu a jami'ar Eastern mediterranean ta kasar Cyprus, ta zargi jakadan Najeriya a kasar Turkiyya, Iliyasu Audu Paragal da cewa ya hana sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II zuwa kasar Cyprus din inda zai halarci wani taron daliban dake karatu a jami'ar Earstern mediterranean da suka saba shiryawa duk shekara.Daliban sun zargi jakadan da cewa ya gayawa sarkin Kano cewa kasar Cyprus ba halastacciyar kasace da aka amince da itaba, wannan dalilin yasa sarkin Kanon ya fasa wannan ziyara da  yayi niyyar kaiwa daliban, daliban sun bayya cewa suna so jakadan ya fito ya musu cikakken bayani akan dalilinshi na yin hakan, dan dalilin difilomasiyya da ya bayar be gamsar dasu ba, domin kamar yanda suka bayyana shi kanshi jakadan yana da 'ya'yanshi dake karatu a wannan jami'a.

Haka kuma sun kara da zarge-zargen cewa ofishin jakadancin Najeriya dake Turkiyya yana amsar damar baiwa dalibai karatu kyauta a jami'ar suna rabawa a tsakin ma'aikatansu kuma suna amsar kudi masu yawa wajan sabunta fasfon dalibai da kuma sa hannu akan shahadarsu.

A karshe sun bukaci Ambasada Iliyasu ya fito ya musu cikakken bayani akan wadannan zarge-zarge da suke mishi.


No comments:

Post a Comment