Thursday, 29 March 2018

Sa'adiya Kabala zata yi Aure

Alamomi masu karfi sun bayyana cewa auren jarumar fina-finan Hausa, Sa'adiya Kabala ya matso wanda ake sa ran za'ayi a watan Afrilu me kamawa idan Allah ya kaimu, saidai wanda zai auri Sa'adiyar be bayyana ba a fili, amma dai a kwanannan ta taba saka wannan hoton na sama inda ta hada hotonta da na wani soja tana mai fatan Alheri.


Ko dashine za'ayi ko kuwa,  sannan kuma a baya ta taba bayyana cewa idan ta taahi yin aure, Adam A. Zangone zai mata waliyyi, shin hakan zai kasance?, lokaci zai bayyana mana.
Wata abokiyar Sa'adiyarce ta saka wannan hoton na sama inda ta rubuta cewa ranar 14 ga watan Afrilu za'ayi auren na Sa'adiya, kuma ta kara da yi mata fatan Allah ya bada zaman lafiya, Sa'adiyar ma ta amsa da cewa Amin.
Muna fatan Allah ya kaimu yasa ayi lafiya.

No comments:

Post a Comment