Tuesday, 13 March 2018

Sai kwararre: Kalli yanda matasan larabawa ke tafiya da mota da taya biyu kawai

Wadannan hotunan yanda wasu matasan larabawa a kasar Saudiyya ke wasan ganganci da mota kenan, matasan na daga tayoyin mota biyu na gefe sannan suyi tafiya da taya biyu kawai.


Shidai wannan wasa ana yinshine ta hanyar samun wani guri me tudu a bi da motar ta kanshi yanda tayoyin zasu daga sama ko kuma a fallo da gudu da motar adan kada sitiyarin yanda tayoyin gefe zasu daga sama sai a cigaba da tafiya da ita a haka.
Matasan larabawan dai sun kware da wannan wasa kuma suna yinshine dan nishadi.
Shidai wannan wasa, kamar yanda rahotanni daga DailyMail ta kasar Ingila suka bayyana, ya samo asaline daga kasar Denmark wanda daga baya kasashe da dama suka dauka kuma akayi amfani dashi a cikin fina-finai da dama.
No comments:

Post a Comment